1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun kashe manoma a Nijar

July 6, 2017

Dakarun gwamnatin Jamhuriyar Nijar sun kashe wasu fararen hula a wani farmakin da suka ce na kuskure na a yankin Abadam da ke kan iyakar kasar da Najeriya.

https://p.dw.com/p/2g64T
Niger Soldaten in Bosso
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Sojoji a Nijar sun halaka wasu fararen hula 14 a wani farmakin kuskurensu da mayakan Boko Haram a yankin Abadam da ke kan iyakar kasar da Najeriya. Wani babban jami'a a yankin, ya ce sojojin gwamnatin Nijar din na sintiri ne a wuraren da aka haramtawa mutane gittawa a yankin na Abadam cikin yankin Diffa, inda suka buda wuta kan talakwan, da aka gano cewa wasu manoma ne.

Biyu daga cikin wadanda sojin suka halaka ne dai 'yan Nijar, sauran 12 kuwa bayanan mahukunta sun ce 'yan Najeriya ne. Lamarin dai na faruwa ne kwanaki uku da mayakan Haram suka kashe mutane tara tare da garkuwa da wasu masu yawa.

Yankin na Diffa dai ya fuskanci hare-hare da kuma artabu tsakanin sojin jamhuriyar ta Nijar da kuma mayakan na Boko Haram.