1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya: An fatattaki sojin Haftar

Gazali Abdou Tasawa
June 27, 2019

A Libiya sojojin gwamnatin Tripoli sun fatattaki sojojin Marechal Khalifa Haftar daga birnin Gharyan wanda Haftar ya kwace a watan Aprilu.

https://p.dw.com/p/3L9Zm
Libyen Kämpfe um Tripolis
Hoto: Imago Images/Xinhua

Rahotanni daga kasar Libiya na cewa dakarun gwamnatin Tripoli wacce kasashen duniya suka amince da ita, sun fatattaki sojojin Marechal Khalifa Haftar daga birnin Gharyan da ke zama babbar hedikwatar rundanar sojojin na haftar da ke a nisan kilomita 100 Kudu maso yammacin birnin Tripoli. 

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito Kakkin gwamnatin ta Tripoli Moustapha al- Meji na cewa bayan fatattakan sojojin na Haftar inda suka halaka gwammai daga cikinsu a lokacin fadan, sun kuma yi nasarar kama 18 daga cikinsu. 

Hotuna da faya-fayen bidiyo na sojojin gwamnatin ta Tripoli suna sinturi a cikin birnin na Gharyan da kuma sojojin Haftar da aka kama yanzu haka suna yawo a shafukan sada zumunta na zamani. 

Masu lura da rikicin kasar ta Libiya na cewa kubucewar wannan birnin na Gharyan wanda sojojin Haftar suka kwace a ranar biyu ga watan Aprilun da ya gabata da kuma ke zama babbar cibiyar samar da kayayyakin bukatu ga sojojin na Janar Haftar, ba karamin koma baya bane ga Janar din a cikin wannan yaki.