1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Nijar sun dakile harin Boko Haram a Diffa

Gazali Abdou Tasawa
May 5, 2020

Sojojin gwamnatin Nijar sun yi nasarar dakile wani gagarimin harin da mayakan Boko Haram suka yi yinkurin kai wa a birnin Diffa a yammacin Lahadin da ta gabata.

https://p.dw.com/p/3bp29
Niger Soldaten
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa sojojin gwamnatin kasar sun yi nasarar dakile wani gagarimin hari da mayakan Boko Haram suka yi yinkurin kai wa a cikin birnin na Diffa mai kunshe da mutun sama da dubu 200. Wasu mazauna birnin na Diffa sun shaida jin aman bindigogi a kudancin birnin na Diffa tun daga karfe hudu da rabi har ya zuwa bakwai na yamma.

Sai dai duk da yake cewa mayakan na Boko Haram ba su yi nasarar shiga birnin na Diffa ba, Kamfanin dillancin Labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa daga bisani kungiyar ta wallafa wani faifayin bidiyo na farfaganda inda ake ganin a tsakiyar gumurzun mayakan na Boko Haram sun yi nasarar kwace wata bindigar madafa da ma wasu motocin yaki a cikin barikin sojan, a yayin da a share daya ake ganin wani sojin a kwance mayakan na Boko Haram na yi masa ruwan harsasai suna kabbara.

 Ofishin ministan tsaro na kasar Nijar ya sanar da fitar da sanarwa kan hari wacce za a wallafa a nan gaba.