1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar Najeriya – zabe ko dai nadi a kananan hukumomi?

Uwais Abubakar Idris M. Ahiwa
October 21, 2024

Sakamakon zabukan kananan hukumomin da aka gudanar a Najeriya na nuna cewa babu wani sauyi da aka samu inda jam'iyyun da ke mulki a jihohin sune ke lashen daukacin zaben shugabanin kanana hukumomi da ma kansiloli.

https://p.dw.com/p/4m3dr
Malaman zabe na wucin-gadi  a Najeriya
Malaman zabe na wucin-gadi a Najeriya Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Bisa tilas ne galibin gwamnonin Najeriya suka gudanar da zabuka a kanana hukumominsu bayan da hukuncin kotun koli da ya tanadar da cewa duk jihar da ta fake da shugabanin riko ba zababbu ba, to ba za a bai wa kananan hukumomin kudadensu kai tsaye ba.

Amma maimakon samun sauyi a tsarin zabukan da ya kamata a gudanar da su bisa dimukurdiyya, sai suka zama dauki dora ne, domin bayan gaza kai kayan  zabe a kan lokaci a jihohi da dama, an rika tilasta wa jami'an zabe rubuta sakamakon zaben da babu shi, inda ake zargin gwamnonin da dauki doran. 

Yadda ake kidaya kuri'un zabe a Najeriya
Yadda ake kidaya kuri'un zabe a NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Watani uku ke nan dai bayan aiwatar da hukuncin da kotun kolin Najeriyar ta yi duk da kafa kwamitin da fadar shugaban Najeriyar ta samar domin aiki da hukuncin, har yanzu babu batun wata karamar hukuma da aka kaiga ba ta kudaddenta kai tsaye.

Zabe ne ko kuwa nadi ake yi a kananan hukumomin kamar yadda aka saba a shekaru fiye da 20 yana faruwa a kasar, abin da ya jefa kananan hukumomi cikin mawuyacin hali domin gwamnonin ne ke shake kudadden nasu.

Duk da hukuncin kotun kolin da aka yi, ana jefa tsoro na abin da ka iya faruwa bisa ga sakamakon zabukan da ka yi a Najeriya.

‘Yan Najeriya musamman mazauna yankunan karkara na nuna tsoron shiga hali na guga ta bayar rijiya ta hana, a baiwa kanana hukumomin kudadden nasu kai tsaye amma gwamnoni su ci gama de yi masu kaka gida.