Simone Gbagbo ta gurfana gaban Kuliya
December 26, 2014Talla
A shekarun 2010 zuwa ta 2011 ne kasar ta tsunduma cikin rikicin na bayan zabe biyo bayan nasarar da shugaban kasar ta Cote d'Ivoire wanda ya yi sandiyyar mutuwar mutane da dama. Gbagbo, wadda ake tsare da ita tsahon shekaru ukun da suka gabata dai, tana fuskantar tuhumar ne a wata kotu da ke Abidjan babban birnin kasar ta Cote d'Ivoire ita da wasu mutane 82, kana kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa da kasa wato ICC da ke birnin "The Heague" na neman ta ruwa a jallo bisa zargin da take mata na aikata laifukan yaki sakamakon rikicin na bayan zabe.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Mohammed Abubakar