Siddi: 'Yan Afirka da aka juya musu baya a Indiya
Kimanin 'yan asalin Afirka dubu 25,000 da aka fi sani da Bantu ne ke rayuwa a dajin Ghats a Indiya. Zuri'ar kabilar Siddi sun isa kasar a matsayin bayi, inda suke rayuwa cikin talauci suke kuma fuskantar kyama.
Raya al'adar kida da rawa
Al'ummar Siddi ba su jefar da al'adarsu ta rawa da kida mai cike da tarihin asalinsu ba. Manuel manomi ne a kauyen Mainalli da ke Karnataka a yankin Uttar Kannada. Ya kan koyar da yara rawa da waka, a kokarinsa na raya al'adar Siddi domin ganin ba ta bace ba. Yana yin hakan a duk lokacin da ya samu lokaci daga aikin noma.
Basirar kera kayayyakin nishadi
A hoton, Besteung da ke zaune a kauyen Mainalli yana kokarin koyar da wani karamin yaro yadda ake buga gangar dammam. Ana amfani da sassaken itace da fatar gada a kera dammam —Bisa al'ada maza ne kadai ke kada gangar yayin da mata ke taka rawa.
'Dhamal'
Chandrika 'yar shekaru 13 da haihuwa na shirin shiga gasar rawar dhamal, rawar al'adar 'yan kabilar Siddi. Ana rawar dhamal cikin nutsuwa inda ake nuna rayuwar 'yan kabilar ta Siddi. Chandrika yar kauyen Mainalli ce kuma ta na matukar son zuwa makaranta kamar yadda ta ke kaunar koyon basirar iya rawar dhamal.
Rawar nishadantar da Sarakuna
David na shirin shiga bikin rawar dhamal. A can baya mafarauta ne ke wannan rawa don bikin murna bayan dawowa daga farauta. Dhamal guda ce daga cikin raye-rayen nishadantar da sarakuna a can baya, yanzu labarin ya sha banbam domin kuwa ana iya taka rawar a yayin bukukuwa.
Aikatau
Wani mai shirya wasan kwaikwaiyo na kasar Singapore da ake nunawa a gidajen talabijin mai suna "Sentuhan Harapan." Ya gwada nuna labarin wani mutum mai suna Ravi da ya bijire wa ubangidansa da ya saka shi yin wani aiki fiye da kudin da ya kamata ya biya shi. Lamarin ya harzuka mai gidan, inda ya lakadawa Ravi duka har da sauran danginsa.
Tsangwama a makarantu
Wani yaro dalibi dan kabilar Siddi a Yellapur, yana bayar da labarin tsangwama da wariyar da ake nuna masa a makaranta, duk a cikin shirin "Sentuhan Harapan." Ya ce sauran yara ba sa so a hada su da 'yan kabilar Siddi, wannan ya sa yara da dama yanke shawarar daina zuwa makaranta.
Kwacen fili
Mahadevi mai shekaru 75 'yar kauyen Karnataka a Magod ce. Mahadevi ta shigar da kara domin ganin an kwato mata filinta da ya kai eka biyar daga hannun wani jami'in gandun daji, wanda ya yi mata karfa-karfa bayan mutuwar mijinta a shekarar 1996.
Nishadi a lokacin hutu
'Yan mata 'yan kabilar Siddi ne a nan ke wasa a kauyen Mainalli, suna lilo a karkashin wata bishiya. Asalinsu 'yan Bantu ne a yankin Kahon Afirka. Tsatson Siddi sun shiga Indiya ne a matsayin bayi a karni na bakwai. Larabawa ne suka fara cinikinsu kafin 'yan kasar Potugal daga bisani Birtaniya ta ci gaba. Akwai wadanda suka shigo ta hanyar kasuwanci ko aikin ruwa.
Nelson Mandela gwarzo abin koyi ga kabilar Siddi
Nelson Mandela shugaban bakar fata na farko a Afirka ta Kudu da ya kawo karshen wariyar launin fata. Hoton na rataye a gidan daya daga cikin 'yan kabilar Siddi a kauyen Talikumbri. Bayan kawo karshen cinikin bayi, 'yan kabilar Siddi sun tsere cikin daji, gudun kada a azabtar da su. Tun wancan lokacin al'ummar da yanzu suka kai kimanin dubu 25,000 ke rayuwa a kebe daga sauran mutane.