Shugabannin duniya sun yi tir da harin da aka kai wa Trump
July 14, 2024Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana harin a matsayin barazaga ga ci gaban dimukradiyya.
Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya ce rigingimun siyasa ta kowace siga ba su da mazauni a tsakanin al'ummar wannan karni.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da ya bayyana harin a matsayin wani bala'i ga dimukradiyya, ya yi wa Trump fatan samun sauki cikin gagawa.
Shi ma a na shi sakon firaministan Canada Justin Trudeau ya ce wannan laifi ne babba da ba za a iya bayyana girmansa ba, kuma ba za a taba lamuntar irin wannan mugun al'amarin ba.
Karin Bayani: FBI ta tabbatar da yunkurin halaka Trump
Fumio Kishida firaministan Japan ya ce dole ne sai duniya ta tashi tsaye a matsayin tsintsiya daya domin yakar duk wata barazana da dimukradiyya ke fuskanta.