Shugaban Zambiya Michael Sata ya mutu
October 29, 2014Gwamnatin Zambiya ta tabbatar da mutuwar shugaban kasar Michael Sata. Tun da farko wata majiyar gwamnati ta shaidawa kafafen yada labarai cewa, gaskiya ne shugaba Sata yarasu a wani asibiti mai zaman kansa dake binrin London, kuma daga bisani sai kakakin majalisar ministoci a hkumance ya yiwa yan kasar jawabin tabbatar da mutuwar. Dama dai tun shekaran jiyawa wasu majiyoyi da ba na hukuma ba, suka fara rade-radin mutuwar shugaba Michael Sata, amma kakakin majalisar ministocin a jawabin da ya yi, yace Sata ya mutu ranar 28.10.2014. Tun kwanaki goma da suka gabata ne dai Michael Sata dan shekaru 77 da haifuwa ya bar kasar izuwa London don yin jinya, inda matarsa da wasu mukarrabai suka yi masa rakiya. Dama tun watannni hudu da suka gabata ne dai, aka fara damuwa kan halin lafiyar shugaban, inda tun lokacin aka daina ganinsa a bainal jama'a.