1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Shugaban Somaliya ya mika wuya

April 28, 2021

Bayan matsin lamba daga ciki da ma wajen kasar Somaliya,gwamnatin kasar ta ce za a dubi yiwuwar shirya zabe da ta janye a cikin makonnin da suka gabata.

https://p.dw.com/p/3sh7r
Somalia Mohamed Abdullahi Farmajo
Hoto: Getty Images/AFP/M. Haji Abdinur

Shugaban kasar Somaliya, Mohamed Abdullahi Farmajo, ya nuna bukatar kasar ta sake komawa kan teburin tattauna batun zabe, wani abu da ke nuna alamun kokari na yin watsi da tsawaita wa'adinsa na mulki da ya yi a ranar 12 ga wannan wata na Afrilu.

'Yan kasar Somaliya da dama ne dai ke ta zanga-zangar adawa da matakin kara wa kansa shekaru biyu da shugaban kasar ya yi, bayan karewar wa'adinsa a hukumance a ranar takwas ga watan Fabrairun da ya gabata.

A wani jawabin da ya yi ta kafar talabijin a Somaliyar, Shugaba Farmajo, ya ce zai bayyana a gaban majalisar dokokin kasar, domin samun sahalewar majalisar game da bukatarsa ta a tsara wa kasar lokacin zaben.

Shugaba Farmajon ya kuma ya ja hankalin jam'iyyun siyasa da su guji yin duk wani abun da ke iya 6ata wannan shiri da ya bijiro da shi.