1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Nigeriya ya kammala rangadin yini biyu a Niger Delta

May 15, 2010

Goodluck Jonathan ya ziyarci yankin Ogoni domin ganin ayyukan raya al'umma dake gudana

https://p.dw.com/p/NOyj
Hoto: AP

Shugaban Tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan ya ƙarasa ziyarar aikinsa na yini biyu a yankin Niger Delta mai arzikin man petur da ziyartar yankin Ogoni. Jonathan ya ziyarci Ogoni dake zama mahaifar mai fafutukar kare muhalli marigayi Ken Saro-Wiwa ne, domin ganin ayyukan raya al'umma da ke gudana a wannan yankin. Ziyarar tasa dai na zama irinta ta farko tun bayan da ya hau matsayin shugaban ƙasa a farkon wannan watan, kuma ta farko a ɓangaren wani shugaban Najeriyar, bayan shirin afuwa da marigayi shugaba Umar Musa Yar'aduwa ya  gabatar ga dubban mayaƙan sakai da suka ajiye makamai a bara.

Mawallafiya: zainab Mohammed Edita: mohammad Nasir Awal