Shugaban Kwango na kan gaba a sakamakon zaben kasar
March 22, 2016Talla
A ta cewar sakamakon da shugaban hukumar zaben kasar Henri Bouka ya fara bayyanawa manema labarai a Brazziville ya yi nuni da cewar sakamakon daga gundumomi 72 cikin 111 na cewar Denis Nguesso ne yayi fintinkau da kuri'un da aka kada.Dole ne dai shugaba Sassou Nguesso ya sami gaggarumin rinjaye a kan abokan takarar takwas muddin dai baya son a kai ga zagaye na biyu na zaben.
A yayin da a cen Jamhuriyar Nijar hukumar zaben kasar CENI ta bayyana cewar shugaba Muhammadu Issoufu ne ya lashe zaben kasar da sama da kashi 90 cikin dari wanda kuma yake cike da rudani bayan kauracewa da 'yan adawar kasar da ke goyan bayan Hama Amadou mai kalubalantar shugaban kasar wanda yanzu haka yake a Faransa domin neman lafiya.