A karon farko shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya halarci Zaman kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa da kasa da ke birnin The Heague na kasar Neatherlands Domin amsa tambayoyi a tuhumar da ake masa bisa zargin haddasa rikicin bayan zabe na shekara ta 2007 zuwa 2008 a kasar ta Kenya.