1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyarar Scholz ta farko a kasar Indiya don karafa hulda

Mohammad Nasiru Awal MAB
February 25, 2023

Wata babbar tawagar 'yan kasuwa na yi wa Olaf Scholz rakiya a ziyararsa ta farko a Indiya tun bayan darewarsa kan kujerar shugaban gwamnatin Jamus.

https://p.dw.com/p/4NyY8
Deutschland Bundeskanzler Scholz in Indien
Hoto: REUTERS

Tare da wata babbar tawagar manyan 'yan kasuwa, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya fara wata ziyara ta farko a kasar Indiya tun bayan darewarsa kan kujerar shugaban gwamnatin Jamus. Gwamnatin tarayyar Jamus na daukar kasar Indiya mai yawan al'umma miliyan dubu daya da ddubu dari hudu ke kuma zama ta biyar a karfin tattalin arzikin duniya, a matsayin wata dama ta fadada huldar kasuwanci da na tattalin arziki ga kamfanonin Jamus, don rage dogaro da kasar Chaina.

Sai dai a huldar siyasa har yanzu da sauran rina a kaba tsakanin kasashen Jamus da Indiya, kasancewa Indiyar ta matukar dogara da makamai da kuma makamashi daga kasar Rasha.

Gwamnatin Indiya karkashin FM Narendra Modi, ba ta fito karara ta yi tir da yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine shekara guda ta gabata ba.