SiyasaAfirka
Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kudin 2024
January 1, 2024Talla
A karon farko tun bayan hawan sa kan karagar mulkin Najeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin kudin kasar na shekarar bana.
Kasafin na Naira Triliyan 28 da sama da biyan 700 dai ya samu kari na Naira Triliyan daya da miliyan dubu dari biyu bisa abun da shugaban ya mika wa majalisun kasar guda biyu a karshe na watan Nuwamban bara.
Akwai dai fata da kuma buri mai girma daga miliyoyin 'yan Najeriyar da ke zaman jiran shugaban da ya dau alkawarin inganta rayuwarsu bayan janye tallafin man fetur a bara.
To sai dai a fadar Atiku Bagudu ministan kasafin kudin, kasafin dan ba ne ga sauyi cikin kasar da ke bukatar hakuri, inda ya fara da bayanin kan kunshin.