Shugaban Rasha Putin:Akwai yiwuwar yakin duniya na 3 da NATO
March 18, 2024Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce ba zai iya cire tsammanin yiwuwar faruwar yaki da kasashen kawancen NATO ba, wanda zai zama silar yakin duniya na uku.
Mr. Putin ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Moscow da yammacin Lahadi, yayin gabatar da jawabin nasarar lashe zaben shugaban kasa, yana mai cewar tuni ya gane cewa sojojin kawancen NATO na cikin Ukraine suna dafa mata, a yakin da aka shafe sama da shekaru biyu ana gwabzawa, har ma an jiyo suna turancin Ingilishi da Faransanci a fagen daga.
Karin bayani:Shugaban Rasha Vladimir Putin ya lashe zaben shugaban kasa
Hukumar zaben Rasha ta ce Shugaba Putin ya samu kaso 88 na cikin 100 na kuri'un da aka kirga, a zaben da babu wani fitaccen 'dan takarar da ke karawa da shi.
Karin bayani:Putin: Mun fi Amirka karfin makaman nukiliya
Tuni dai shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya mika sakon taya murnar lashe zaben ga Shugaba Putin.