Shugaba Koroma na Saliyo ya sake samun nasara
November 24, 2012Shugaban ƙasar Saliyo Ernest Koroma, da aka sake zaɓa cikin wa'adin mulki na biyu, ya yi alƙawarin ci gaba da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar wadda ke farfadowa daga yaƙin basasa.
Koroma ya samu kashi 58 cikin 100 na kuri'un da aka kaɗa cikin zaɓen makon jiya, ya doke abokin karawarsa tsohon shugaban gwamnatin mulkin soja Julius Maada Bio, wanda ya samu kashi 37 cikin 100. Kuma masu ido kan zaɓe na ƙasashen duniya sun yaba da yadda aka gudanar da zaɓen.
A wannan Jumma'a aka rantsar da Koroma a matsayin shugaban na Saliyo, domin wa'adi na biyu, kuma ya nemi haɗin kai daga 'yan adawa. Bisa tsarin ƙasar ta Saliyo, ɗan takara na buƙatar samun fiye kashi 55 cikin 100 kafin kaucewa zuwa zagaye na biyu na zaɓe, abun da shugaba Koroma ya samu. Cikin shekara ta 2002 aka kawo ƙarshen yakin basasan ƙasar ta Saliyo da ke yankin Yammacin Afrika.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh