1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Idriss Deby ya dakatar da Ministoci uku a Majalisar zartarwa sa.

August 28, 2006
https://p.dw.com/p/BulO

Shugaban ƙasar Chadi Idriss Deby Itno ya dakatar da ministan albarkatun mai da kuma wasu ministoci biyu a majalisar zartarwar ƙasar waɗanda suka ƙulla yarjejeniya da kamfanonin mai biyu na ƙasashen ƙetare, wato Chevron da kuma Petronas waɗanda ya umarce su da su fiye daga ƙasar saboda ƙin biyan harajin gwamnati. Shugaba Idriss Deby ya dakatar da ministocin uku ne bisa zargin su da almundahana tare da kamfanonin man. A ranar Asabar ɗin data gabata ce shugaban ƙasar ya umarci kamfanonin man biyu da su tattara ya nasu ya nasu su fice daga ƙasar Chadi. Sai dai kuma wata majiya daga kakakin shugaban ƙasar Hourmadji Moussa Doumgor yace mai yiwuwa ne a ɗauki yan kwanaki kafin kamfanonin su kammala kwashe kayayykin su domin bin umarnin. Kamfanonin biyu na Chevron da Petronas har ya zuwa wannan lokaci basu maida martani a game da matakin gwamnatin na korar su daga ƙasar ba.