Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu zai karbi rantsuwa
June 19, 2024A Larabar nan ce shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu zai karbi rantsuwar kama aiki a zango na biyu na mulkinsa a birnin Pretoria, bayan da jam'iyyarsa ta ANC ta amince da kafa gwamnatin hadaka da 'yan adawa, sakamakon gaza samun rinjayen da zai bata damar jagorantar kasar a zaben da ya gabata.
karin bayani:Babbar jam'iyyar adawar Afirka ta Kudu ta amince da marawa shugaba Cyril Ramaphosa
Manyan bakin da za su halarci taron sun hada shugabannin kasashe kusan 20 na duniya, da suka hada na Chaina da Masar da Cuba da Zimbabwe, da Najeriya, sai Angola da Falasdinu da ma sauran bakin da aka gayyata daga sassa daban-daban na duniya.
karin bayani:Manyan 'yan takara a zaben Afirka ta Kudu
Jam'yyun da ANC ta yi hadaka da sun hada da Democratic Alliance DA, da mafi akasarin mamobinta farar fata ne, da Inkatha Freedom Party mai kaifin kishin kabilar Zulu, sai mai kyamar baki ta Patriotic Alliance, da kuma GOOD party.
Ana sa ran jin sanarwar mukarraban gwamnatinsa jim kadan bayan shan rantsuwar.