Shugaba Ali Bongo ya bayyana abainar jama'a
August 19, 2019Talla
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar yayin taron manema labarai da ta gudanar. Matakin fitar da sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da kawancen 'yan adawa ke bayyana shugaban dan shekaru 60 da ke fama da rashin lafiyar shanyewar wani bangare na jiki, da cewa ba ya iya tafiyar da harkokin mulki.
Kwana guda gabanin sanarwar dai an hangi Shugaban Ali Bongo a bainar jama'a, yana dogara sanda a yayin da yake jagorantar bukin tunawa da ranar samun 'yancin kan kasar.