Shugaba Biden ya kamu da Corona
July 22, 2022Talla
Shugaban Amirka Joe Biden ya kamu da kwayar cutar Corona, kamar yadda fadar White House ta tabbatar.
Shugaba Biden wanda ke da shekaru 79 a duniya, ya harbu da Coronar ne bayan sakamkon gwajin da ya yi ya tabbatar da hakan.
Shugaban na Amirka ya ce akwai wasu kananan alamun cutar a tare da shi, sai dai kuma ba ya jin wata gagarumar rashin lafiya a yanzu.
Tuni kuma ya ce ya fara shan maganin cutar mai suna paxlovid.
Likitan shugaban na Amirka, Dr. Kevin O'Connor, ya ce Mr. Biden na fama da kasala da mura gami da tari ne tun da yammacin ranar Laraba.