Shirye shiryen zaben shugaban kasa a Gabon
October 20, 2005Hukumar zabe mai zaman kanta, a Gabon ta tace, sunayen yan takara 4, daga jerin yan takara 13, da su ka bukaci shiga zaben shugaban kasa, da za a yi ranar 27 ga watan november a kasar.
Yan takara 4, da hukumar zabe mai zaman kanta, ta amince da su , sune shugaba mai ci yanzu Omar Bongo Ondimba, dan takara a karkashin tutur jam´iyar PDG, mai rike da ragamar mulki, da Mambundu Pierre, dan takara jam´iyar UPG,, mai adawa, da kuma Myboto Zacharie , da Tomo Ernest ,dukan su 2, yan takara indipenda.
Shugaban hukumar zabe mai tzaman kanta, Gilbert Gulakia, a wani taron manema labarai da ya shirya, ya sanar cewa, sauran yan takara 9, da takardun basu samu shiga ba,su na da yancin daga kara, ga kotun koli, wace ke da alhakin yanke hukunce karshe.
Mafi yawa daga yan takara da aka yi wasti da su yabn inmdipenda ne , kuma akasarin su sabin shiga ne a fagen siyasar Gabon.
Dan takara Myboto Zachari, da farko, na daya daga aminnan kut da kut na shugaban Omar Bango, kamin daga bisani su zama hannun riga.
Shi kuwa Pierre Mambundu, cemma, ya fafata a zaben shekara ta 1998 tare da shugaga Omar Bango.
Masu kulla da harakokin siyasa a Gabon, na hasashen cewa, babu ko ja,El haji Omar bango, za shi kara tazarce karo na 6.
Dan shekaru 69 a dunia Omar Bango, ya hau karagar mulkin kasar Gabon tun 1967.
A halin yanzu, shine shuagaban kasa wanda ya fi dadewa bisa karagar mulkin a nahiyar Afrika baki daya, tun baya mutuwar Yasimbe Yadema na Togo a watan Februaru da ya wuce.
An haifi Omar Bango ranar 30 ga watan desember shekara ta 1935 a garin Bateke da ke kudu masu gabanci kasar, ya kuma yi karantun sa, a Brazaville, wace a lokacin ke matsayin babban birnin yankin Afrika ta tsakiya.
Bayan yayi aikin bautar kasa, a Cyadi, shugabn kasar Gabon na lokacin Leon Mba ya nada shi, daraktan fadar sa.
Yakuma rike matsayin minister, a shekara ta 1965, kamin ya zama mataimakin shugaban kasa a shekara ta1967.
Shugaban kasa Leon Mba ya kwanta dama ranar 28 ga watan november na shekara ta 1967 abinda ya baiwa Omar Bango damar maye gurbin sa.
Shekara guda bayan hawan sa mulki, ya kafa dokar jam´iya daya tillo, a kasar da ya ke jagoranta.
A shekara ta 1973, ya musulunta, ya kuma cenza suna daga Albert Bernad Bongo, zuwa El haji Omar Bongo.
Bayan kadawar iskan demokradiya a shekara ta 1990 a nahiyar Afrika, Omar Bango ya bada dammar girma jam´iyu da dama a kasar Gabon
A sakamakon zaben shugaban kasa da a kayi a shekara ta 1993, ya samu rinjaye da kashi 51 bisa 100 na kur´iun da a ka kada sannan a shekara ta 1998, ya kara tazarce, da kashi kussan 66 bisa 100.
A wannan karo masu kulla da harakokin siyasa, a Gabon,na tabbatar da cewa za shi kara zarcewa,a dalili da rarabuwar kanu da ya hadasa a tsakanin jamiyun adawa.