1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen jana'izar Nelson Mandela

December 7, 2013

shugabannin kasashen duniya da dama ciki har da na Amirka sun tabbatar da cewa za su halarci jana'izar marigayi tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela.

https://p.dw.com/p/1AUdq
Hoto: Reuters

Fadar gwamnatin Amirka ta White House ta sanar da cewa Barack Obama, da ya kasance shugaban kasar Amirka bakar fata na farko zai tashi zuwa Afirka ta Kudu a makon gobe tare da mai dakinsa Michelle Obama, domin shiga sahun sauran takwarorinsa na duniya wajen halartar adduo'i na musamman na tunawa da marigayi Nelson Mandela, da za a gudanar a ranar 10 ga watan Disambar nan da muke ciki.

Shi ma tsohon shugaban kasar Amirka George W. Bush da mai dakinsa Laura Bush za su tashi zuwa Afirka ta Kudun tare da Obama. Yayin da Bill Clinton, da ya ke kan karagar mulki a lokacin da Nelson Mandela ya zamo shugaban kasar Afirka ta Kudun, shi ma ya sanar da cewa ya na shirin tafiya da iyalansa domin halartar jana'izar.

Firaministan kasar Australia Tony Abbott ya ce zai halarci jana'izar gwarzon shugaba na duniya da ya bayyana da mai nagarta ta gaskiya, yayin da a hannu guda kuma shugaban kasar Brazil Dilma Rousseff, ta kasance cikin sahun shugabannni kasashen duniya da za su isa Afirka ta Kudu a mako mai kamawa.

Bayan kammala aduo'i ga marigayi Nelson Mandela, daga bisani za a kai gawarsa zuwa kauyensu na Qunu a ranar Jumma'a mai zuwa idan Allah ya kaimu, domin yi masa jana'iza a ranar Lahadi 15 ga wannan wata na Disamba da muke ciki.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe