Ghana: Shirye-shiryen gudanar da zabe
November 20, 2024Talla
A dukkanin jihohin kasar aikin ya wanzu ne a karkashin jagorancin Hukumar Zaben da hukumomin tsaro da wakilan jam'iyyun da za su fafata da juna a zabukan. Kawo yanzu babbar jam'iyyar adawar gwamnati ta NDC ta nuna gamsuwarta ga matakan da Hukumar Zaben ta saka na kare kayayyakin zaben a kasar. Manazarcin al'amuran siyasa Sadik Abdul Latif ya ce ba a nan take ba, domin bayan wannan shirin akwai jan aiki na tabbatar da tsaron kayan kafin ranar zaben da ma bayan zaben. Wannan dai mataki ne da Hukumar Zaben Ghana ta saba dauka, a duk lokacin gudanar da zabe.