1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-Shiryen gudanar da zaɓe a Zambiya

September 19, 2011

Zambiya ta shirya gudanar da zaɓen shugaban ƙasa wanda manazarta suka bayyana a matsayin zabe mafi zafi a tarihin zaɓukan ƙasar

https://p.dw.com/p/12cCu
Shugaba mai ci Rupiah Banda kuma ɗan takarar jamiyyar MMDHoto: dapd

Al'ummar Zambiya zata gudanar da zabe a karo na shidda, ranar 20 ga watan Satumba, inda za ta zaɓi shugaban aƙsa da 'yan majalisa da kansiloli. Manazarta sun kwatanta zaɓen wannan karon, a matsayin takara mafi zafi a tarihin zaɓukan kasar. Haka nan kuma ƙaruwan adadin manya-manyan 'yan kasuwan China a fanin tattalin arziƙi, ya kasance kan gaba a mahauwarorin yaƙin neman zaɓen jamiyyun ƙasar.

'Yan takarar shugabancin ƙasar guda goma sun ɗauki lokaci suna kewaya ƙasar domin zawarcin ƙuri'un al'umma a zaɓen a kowani mataki. To sai dai 'yan takarar sun mayar da hankali wajen sukan lamirin juna da kuma amfani da kalaman ɓatanci inda shugaba mai ci, kuma ɗan takarar jamiyyar MMD Rupiah Banda ya zargi abokin Hammayar sa Michael Sata na Jamiyyar Patriotic Front da goyon bayan masu luwaɗi da maɗigo a yayin da shi kuma Michael Sata ya rama da cewa Banda na taimakawa China wajen mamaye al'amurar da suka shafi tattalin arzikin ƙasar. Isaac Kabela, mallami ne a jamiar Zambiya:

Sambia Wahlen 2011
Hoto: picture alliance/landov

"A gani na mahauwarorin ba'a yin su bisa ƙwararan manufofi ana yin su ne da nufin ɓatawa juna suna. A matsayi na na mai nazari a kan al'amurar siyasa, zan ce ba haka siyasa take ba saboda muna maganar sauyi ne kuma ba zamu iya sauya al'umma ba idan muka mayar da hankali a kan halayyar mutane a maimakon batutuwa da suka shafi tattalin arziƙi, zamantakewa da al'adun da duk wanda aka zaɓa zai fuskanta kuma a gani na irin abunda ke kawo sauyi ke nan"

Dangantakar China da Zambia ta taka rawa sosai a mahauwarar yaƙin neman zaben kasancewar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu ya cigaba da ƙaruwa zuwa fiye da kashi 30 cikin 100 tun daga shekara ta 2000. A shekarar 2010 ma an kwatanata darajar cinikayyen da tsaban kuɗi dallan Amurka billiyan biyu da rabi. Yawancin 'yan Chinan da ke zuba jari a ƙasar suna adawa da kafa ƙungiyoyin ƙwadago, kuma ana zarginsu da saɓawa dokokin ƙwadago da nuna halin ko in kula. Ko a bara masu zuba jari a ayyukan wata mahakar Kwal da ke Collum sun bindige wasu mahaƙa guda 17 bayan da suka nuna adawa da irin yanayin da suke aiki.

Shi dai Banda ya yi alƙawarin ƙara shirye-shiryen raya ƙasa inda ya fitar da wani shiri mai ƙudurori bakwai na inganta tattalin arziƙin ƙasa, a yayin da shi kuma Sata wanda ake zarginsa da kare manufofin Robert Mugabe na zimbabwe a fili, wanda kuma ya kasance tsohon minista a gwamnati mai ci kafin ya canza sheƙa ya yi alƙawarin rage kuɗin haraji. To sai dai Neo Simutanyi ya ce akwai batutuwan ma da suka fi waɗannan tayar da hankali

Sambia Wahlen 2011
Hoto: picture alliance/ZUMA Press

"akwai raɗe-raɗin cewa jamiyyun adawa musamman ma Patriotic Front ba za su amince da sakamakon zaɓen da zai nuna cewa basu yi nasara ba, a gani na wannan na da haɗari saboda muna amfani da tsarin lashe zaɓe da ƙanƙanin rinjaye kuma a irin wannan lamarin zai yiwu jamiyya ta yi rinjaye da ƙuri'u kalilan"

Tuni dai Darektan hukumar zaɓe madam Priscilla Isaac ta sanar da cewa sun yi tanadin duk abubuwan da ake bukata ma zaɓen na bana kuma an baza kimanin ma'aikata dubu 60 a mazaɓu 150 na ƙasar don tabbatar da sahihin zaɓe.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Yahouza Sadissou Madobi