Shirye-shiryen bikin cikar Mandela shekaru 95 a duniya
July 17, 2013Yayin da a ranar Alhamis tsohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela zai yi bikin cikarsa shekaru 95 da haihuwa a kan gadon asibiti inda ake masa magani, duniya na ci gaba da yi masa fatan alheri tare da gudanar da ayyuka na gari. A Afirka ta Kudu kungiyoyin masu hawa keke za su yi aikin gayya na share tituna sannan masu aikin sa kai za su yi fentin makarantu yayin da su kuma a nasu bangare 'yan siyasa za su sadaukar da mintoci 67 don gudanar da muhimman ayyukan agaji don girmama shekaru 67 da Mandela yayi yana yi wa jama'a aiki. A shekarar 2010 Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana ranar haihuwar Mandela, wanda ya taba samun kyautar zaman lafiya ta Nobel, a matsayin ranar Mandela, amma ga da yawa bikin na bana na da matukar muhimmanci. Mandela dai ya shafe makonni shida da suka gabata a wani asibitin birnin Pretoria inda har yanzu yake fama da matsanancin rashin lafiya ko da yake an ce babu abin fargaba a ciki.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu