A cikin shirin za a ji cewa gamayyar kungiyoyin fararan hulla a Nijar sun gudanar da jerin gwano gami da taron gangami a birnin Yamai da ma sauran wasu biranen kasar, inda suke bukatar gwamnati da ta janye sabuwar dokar kasafin kudin kasar ta 2018 ta suka ce za ta muzgunawa rayuwar al'umma.