A cikin shirin za a ji Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta gudanar da taron neman mafita dangane da matsalolin da ta ke fuskanta na cikin gida. A jamhuriyar Nijar kuwa wani takon saka ne ya kunno kai tsakanin kungiyar alkalai ta SAMAN da gwamnati dangane da nade-naden mukamai da canza guraben aikin alkalan, inda kungiyar ke zargin gwamnatin da nuna mata wariya.