A cikin shirin za a ji cewar a kasar Kamaru, magoya bayan jam'iyya mai mulki ta Shugaba Paul Biya sun kai ziyarar yakin neman zabe yankin da ke amfani da turancin Ingilishi duk da barazanar da ake fuskanta daga bangaren 'yan aware. A jamhuriyar Nijer ana takun saka tsakanin kungiyoyin dake kula da asibitoci na COGES da kuma gwamnati.