A cikin shirin za a ji cewa manazarta harkokin siyasa na yaba tsarin mika jan ragamar mulkin kananan hukumomi ga talakawa, a yayin da a jihar Katsina ta Najeriya gwamnatin jihar ta sanar da cire wa ma'aikatan jihar wani kaso na albashinsu da zummar sake gina babbar kasuwar jihar da gobara ta lalata.