Shirin ya kunshi halin da 'yan kasuwar birnin Katsina ke a ciki bayan asarar dumbin dukiya sakamakon wata mummunar gobara. A Nijar ra'ayoyi ne ke bin alwashin sabon Shugaba Bazoum Mohamed, a kan koma bayan harkokin ilimi a kasar. Akwai matsayar da aka cimma game da yarjejeniyar Nukiliyar Iran.