A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya, kungiyar Amnesty International na neman a dauki matakin gaggawa domin kawo karshen gallazawa daliban makaranta ta hanyar horo mai tsanani. Za kuma a ji yadda kasar Libiya ta tasa keyar gomman 'yan Najeriya zuwa gida da nufin tsananta dokoki kan bakin haure.