A cikin shirin za a ji cewa, wata kotu a Indiya ta yankewa shahararren jarumin fina-finan Bollywood Salman Khan hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar bayan da ta same shi da laifin farautar na'uin wata dabba da ke barazanar bacewa daga doron kasa.