A cikin shirin za a ji cewa gwamnatin Jamus, ta kai wa 'yan gudun hijira da ke yankin Diffa da rikicin Boko Haram ya dai-daita taimakon kudi Euro miliyan daya da dubu 700 ta hanyar kungiyar bada agajin gaggawa ta kasa da kasa CICR a ofishinta da ke a birnin Yamai.