Shirin bunkasa tattalin arzikin Najeriya
May 10, 2016Jihar Katsina dai ita ce ta biyu baya ga jihar Kaduna da ta yi wannan yunkuri na sama wa kanta hanyoyi da za su bata kudaden shiga inda ta dukufa wajen jan hankalin masu zuba jari musamman ma dai a fannonin da suka danganci noma da ma'adinai ta yadda jihar za ta samu kafofi na dogaro da kan ta maimakon jiran kudi daga gwamnatin tarayya.
Domin samun nasarar wannan yunkuri nata, jihar ta Katsina ta kira wani taron koli wanda aka bude shi a wannan Talatar (10.05.2016). A wajen bude taron ne ma shugaban Najeriya din Muhammadu Buhari ya ce jihar ta kama hanyar cimma kudurin da ya ke da shi na kawar da matsalar fatara da rashin aikin yi wanda a iya cewa ya zama kamar jamfa a Jos.
Kamfanoni da dama daga ciki da wajen Nijeriya ne dai ke halartar wannan taro inda wasu daga cikinsu suka nuna sha'awar saka jarinsu a fannonin noma musamman na kayan lambu irinsu Tumatir yayin da wasu kuma suka ce suna son maida hankali ne a fannonin ma'adinai irinsu Zinari da Lu'u-Lu'u da makamantansu.
Guda daga cikin 'yan kasuwar da suka halarci taron wato Mr. Olu Ayuba na kamfanin Secure Technical Roles da ke kasar Spain ya ce dama sun jima suna son shiga jihar ta Katsina don zuba jari a fannin makamashi da ake samuntawa kuma hakan zai taimaka musu wajen samar da wadatacciyar wutar lantarki a jihar idan komai ya tafi kamar yadda suka tsara.
Baya ga wannan kamfani na kasar ta Spain, wasu karin kamfanoni kimanin sama da 33 daga Amirka da Turai da Asiya ne ke halartar taron yayin da a cikin Najeriya kuma kusan dukkan manyan kamfanonin da ke kasar ne ke halartar taron ciki kuwa har da kamfanin Dangote.