GAT
July 15, 2019Talla
Gabanin taron koli na Kungiyar AU da ya gudana a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar kan batun yarjejeniyar kasuwanci maras shinge a Afirka, kungiyoyin mata da ma masu ruwa da tsaki a al'amuran matan a Afirka, sun gudanar da wani taro a kasar ta Nijar, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi matsalolin matan Afirka tare da fito da shawarwari na shawon kansu, shawarwarin da kuma suka gabatar da su ga taron na AU domin a share wa matan hawayensu.