Shekaru biyu da fara hako man fetur a Nijar
November 28, 2013Ranar 28 ga watan Nowambar 2011 ne Nijar ta shiga sahun kasashen duniya da ke da arzikin man fetur, bayan kaddamar da matatar mai da aka fi sani da suna SORAZ a Damagaram. An shirya za ta dinga bayar da ganga dubu 20 na fetur a kowace rana ta Allah domin amfanin al'umar kasar tare da sayar da shi ga wasu kasashe makwabta.
Sai dai wannan batu na ci-gaba da haifar da muhawara a tsakanin gwamnatin da 'yan kasar dangane da tasirin da samun wannan arziki ya yi ga tattalin arzikin Nijar dama rayuwar al'umarta. Malam Nouhou Arzika shugaban kungiyar farar hula ta MPCR na ganin cewa ya zuwa yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Ya ce "Burin da muka yi na kasa ta yi amfani da wannan man fetur da Nijar ta samu domin mu daina zuwa bara, haka ba ta cimma ruwa ba. Kudin da suka samu sai kawai anan hada hada: magabata ne su ke kirkiro da hanyoyin satar kudi.a Ayanzu haka akwai sabbin masu kudi da aka samu a cikin gwamnati da wasu sauran manyan hukumomi da aka sanya. "
Ra'ayoyi sun sha ban-ban kan man fetur a Nijar
Kusan al'umar Nijar baki daya ne suka kasance a cikin farin ciki a lokacin kaddamar da wanann aiki na soma hako man fetur kasar tasu. Sai dai wani mazunin birnin Yamai ya ce " har yanzu ba mu gani a kasa ba. Abun da muka saba sha a kullum,har yanzu haka shi muke ci-gaba da sha mu talakawa." Sai dai wani dan Nijar da DW ta tattauna da shi ya nuna gamsuwarsa a kan man fetur, inda ya ce "kullum man fetur ba ya yankewa a kasuwa, har ma a kauyuka ana samunshi."
Gwamnati ta ce an fara cin gajiyar fetur a Nijar
A lokacin da ya ke mayar da martani a kan wadannan korafe- korafe, ministan da ke kula da harkokin man fetur na Nijar Foumakoy Gado ya nunar da cewa a zahiri NIjar na amfani da arzikin karkashin kasa da Allah ya hore mata. Ya ce " A shekarar da ta gabata ganga dubu 12 kawai muke samu a kowace rana, amma a wannan shekara, kudaden da wanann aiki ya shigar aljihun gwamnati ya kai miliyan dubu 94 kuma a bana muna sa ran za a kai miliyan dubu 100 ko 110."
Wasu sabbin bincike da aka gudanar a Nijar a baya-bayan nan a yankin Agadem ya nunar da cewa yawan fetur da aka gano ya tashi daga ganga miliyon 300 zuwa ganga miliyon 600 a shekara. Kuma ana sa ran cewa zai kai ganga miliyan dubu nan da wani lokaci. Hakazalika a cikin yankin Tenere da Bilma bincike ya gano cewa akwai wani karin man fetur da ke binne a cikinsu.
Mawallafi: Gazali Abdou Tasawa
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe