1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin yankin Sahel ya mamaye jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal SB
January 17, 2020

Cika shekaru 50 da kawo karshen yaki basasa a Najeriya ya dauki hankalin jaridun Jamus gami da taron neman hanyoyin dakile rikicin yankin Sahel.

https://p.dw.com/p/3WM9d
Bildergalerie Biafra-Krieg | Hilfe
Hoto: picture-alliance/Leemage/MP/Lazzero

A wanna makon za mu fara sharhi da labarun jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka tarayyar Najeriya inda a  tsakiyar wannan mako wato ranar 15 ga watan nan na Janeru aka cika shekaru 50 cir da kawo karshen yakin basasan kasar da aka fi sani da yakin Biafra. Ta ce shekaru 50 da suka gabata aka kawo karshen yakin neman ballewar yankin Kudu maso Gabashin Najeriya don kafa kasar Biafra, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da aka kiyasta yawansu ya kai tsakanin dubu 500 zuwa miliyan uku. Ta ce a ranar 6 ga watan Yulin 1967 aka fara yakin a kuma kawo karshensa a ranar 15 ga watan Janerun 1970.

Nigerianische Truppen nähern sich der Hauptstadt von Biafra Umuahia 1969
Hoto: Imago Images/United Archives International

Jaridar ta ce a hukumance ba a daukar batun da wani muhimmanci a Najeriya, sai dai yana nan a zukatan mutane musamman al'ummar Igbo, da ke korafi har yanzu ana mayar da su saniyar ware a harkokin tafiyar da kasar, musamman kasancewa har yanzu Najeriya ba ta yi wani shugaban kasa daga wannan al'umma ba. Jaridar ta ce ya kamata a rika fadawa na baya labarin yakin maimakon a yi ta rufa-rufa, wanda hakan ba alheri ba ne domin ba za su san illar yaki ba, balantana su nemi hanya hana sabon rikici na basasa aukuwa. Rufe labarin yakin shi ke kawo bullar kungiyoyin fafatuka irin su IPOB da ke da rajin farfado da akidar Biafra.

Frankreich G5-Sahel Gipfel in Pau
Hoto: DW/F. Tiassou

Zaman makoki da alhini a cikin yanayi na tarzoma, wannan shi ne taken labarin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta buga, inda ta mayar da hankali kan yankin Sahel mai fama da ayyukan ta'addanci. Jaridar ta ce shugaban Faransa Emmanuel Macron na bukatar cikakken hadin kai da shugabannin yankin na Sahel da taimakon kungiyar Tarayyar Turai don yakar ta'adda, a daidai lokacin da al'ummomi a yankin ke kara yin fushi. Jaridar ta ce a kan haka Shugaba Macron ya kira taro a birnin Pau na kasar Faransa, don nunawa a fili cewa bai kamata a rika kallon yaki da ta'addanci a yammacin Afirka a matsayin batu ne na Afirka da Faransa kadai ba. Matsala ce da ta shafi kowa da kowa, wadda kuma ya zama dole a yi mata taron dangi don ganin bayanta.

Sudan Khartum | Sicherheitskräfte
Hoto: picture-alliance/AP Photo/N. El-Mofty

A karshe za mu sake komawa ga jaridar Die Tageszeitung wadda ta yi tsokaci kan boren da wasu sojoji suka yi a kasar Sudan. Jaridar ta fara da cewa shirin aiwatar da sauye-sauye a Sudan na cikin hadari. Ta ce wasu jami'ai na hukumar leken asirin kasar sun yi boren adawa da shirin yi wa rundunar tsaron kasa kwaskwarima. Jaridar ta boren da aka yi ranar Talata a barikokin biyu na hukumar leken asiri Sudan, NISS, da ake matukar tsoronta, na zama babbar shaida cewa, akwai doguwar tafiya kafin zaman lafiya da kwanciyar hankali su dawo a kasar, duk da kawar gwamnatin mulkin kama karya ta Shugaba Omar al-Bashir. Sabbin mahukuntan Sudan na kokarin yi wa rundunar sojin kasar kwaskwarima, amma suna cin karo da turjiya, musamman daga magoya bayan tsohon shugaban kasa da ke korafi za a mayar da su saniyar ware. Saboda haka dole Firaminista Abdallah Hamdok da gwammatinsa su yi taka tsantsan a matakan kawo gyara a cikin kasar, inji jaridar.