Tunawa da bala'in Tsunami
December 26, 2019Talla
Mutane 228.000 ne dai bala'in na tsunami ya yi sanadiyar rasuwarsu baya ga dinbin asarar dukiyoyi. A Lardin Aceh na kasar Indonesiya inda wadanda suka rasa rayukansu a bala'in suka fi yawa, mutane na kai ziyara kaburburan 'yan'uwa da abokan arziki. Bala'in na Tsunami da ya afku a ranar 26 ga watan Disambar shekara ta 2004 dai, na zaman bala'in girgizar kasa ta karkashin teku mafi muni a tarihin duniya. Wannan bala'in dai ya ritsa da yankuna da dama a kasashen Indonesiya da Indiya da Thailand da kuma Sri Lanka.