1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iyalan fasinjojin jirgin Malesiya na jiran tsammani

Lateefa Mustapha Ja'afarMarch 8, 2015

Firaminstan Malesiya Najib Razak ya bayyana cewa ƙasar za ta ci gaba da laluben jirgin saman ƙasar da ya yi ɓatan dabo mai lamba MH370 yau tsahon shekara guda ke' nan.

https://p.dw.com/p/1EnFU
Iyalai na sanya hannu akan hoton jirgin Malesiya da ya bace
Iyalai na sanya hannu a kan hoton jirgin Malesiya da ya baceHoto: Reuters

Razak wanda ya yaba wa tawagar da ke laluben jirgin saman mai ɗauke da mutane 239, ya ce yana da kyakkyawan fatan cewar za a gano shi. Wannan na na zuwa ne a dai-dai lokacin da Firaministan Ostreliya Tony Abbott wanda ƙasarsa ke jagorantar binciken ke cewa akwai yiwuwar su ƙara faɗaɗa bincikensu in har ba a cimma nasara ba cikin sakamakon binciken da suke da shi a hannu a yanzu haka. In dai ba a manta ba jirgin saman kirara Boing 777 mai lamba MH370 ya ɓace ne a ranar takwas ga watan Maris ɗin shekarar da ta gabata ta 2014 ɗauke da mutane 239 a kan hanyarsa ta zuwa Beijing na ƙasar China daga birnin Kuala Lumpur na Malesiyan. A wannan Lahadin ne dai za a fitar da rahoton binciken da aka gudanar dangane da ɓacewar jirgin, da ake kyautata zaton ya faɗa a tekun Indiya.