Shari'ar shugaban Kenya a gaban kotun ICC
November 26, 2013Kotun hukunta manyan laifukan yaki da ke birnin The Hague na kasar Holland ta sanar da cewar, tilas ne shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya ya rinka halartar zaman sauraron shari'ar da ta shafeshi a gaban kotun, muddin dai ba ta bashi damar kauracewa zaman ba, bayan ya nemi izini. Kotun ta yanke wannan shawarar ce yayin zaman da alkalan suka yi a wannan Talatar, a wani abin da ake ganin zai kara dagula dangantakar da dama ta yi tsami a tsakanin hukumomin kasar ta Kenya da kuma na gwamnatocin kasar Afirka - a hannu guda, kana da kotun a daya hannun.
Shugaba Uhuru Kenyatta da kuma mataimakinsa William Ruto dai, na fuskantar tuhumar da ta shafi aikata manyan laifuka a kan bil'Adama saboda rawar da suka taka a rigingimun da suka biyo bayan zabukan kasar a shekara ta 2007, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane dubu daya da 200. Dama dai alkalan da ke sauraren shari'ar manyan jami'an biyu, na amsa bukatun da suke gabatar musu na rashin halartar zaman kotun, domin gudanar da wasu manyan ayyukan da suka shafi ofisoshinsu a cikin gida da kuma wajen kasar.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe