1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar Ntaganda da halin da ake ciki a Afirka ta Tsakiya

Mohammad Nasiru AwalSeptember 4, 2015

Shari'ar da aka fara yi wa tsohon madugun 'yan tawayen Kwango Bosco Ntaganda a kotun ICC da sabon kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/1GRNr
Niederlande Internationaler Gerichtshof Prozess Bosco Ntaganda Den Haag
Hoto: Reuters/M. Kooren

Jaridar Die Tageszeitung ta fara ne da cewa madugun haulolin yaki Bosco Ntaganda ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa, lokacin da kotun ICC da ke birnin The Hague ta fara shari'ar kan aikata laifin yaki, inda ta bude zaman da karanta tuhume-tuhume 18 da ake wa Ntaganda wanda ake wa lakabi da Terminator. Masu shigar da kara na zargin Ntaganda da ya kasance jagoran kungiyar FPLC da ke zama bangaren soji na kungiyar 'yan tawayen UPC da hannu a kisan kare dangi da aikata laifukan yaki tsakanin shekaraun 2002 da 2003 a lardin Ituri da ke Arewa maso Gabashin Kwango.

Babbar dama ga kotun ICC

Bosco Ntaganda Prozess ICC Den Haag 10.01.2014 Bensouda
Fatou Bensouda babbar mai shigar da kara a kotun ICCHoto: Reuters

Rashin imani na Terminator inji jaridar Süddeutsche Zeitung lokacin da take sharhi kan shari'ar da ake wa madugun 'yan tawayen na Kwango Bosco Ntaganda. Ta ce bayan kwan-gaba kwan-baya da kotun ta kasa da kasa mai hukunta laifukan yaki ta yi ta fama da shi a watanni baya, yanzu wannan zaman shari'ar zai ba ta damar wanke sunanta. A karshen shekarar 2014 a dole kotun ta yi watsi da shari'ar da ake wa shugaban Kenya Uhuru Kenyatta saboda rashin isassun shaidu. Hakazalika a watan Yuni shugaban Sudan Omar al-Bashir ya tsallake siradi a Afirka ta Kudu duk da sammacin kama shi da kotun ta bayar bisa zargin aikata kisan kare dangi.

Sabon tsarin mulki don daidaita al'amura

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a wannan makon ta mayar da hankali ne kan sabon daftarin kundin tsarin mulkin kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da nufin kawo karshen rikicin siyasa a kasar.

Versöhnungsforum in Brazzaville
Zaman wani taron sulhu na Afirka ta Tsakiya a birnin Brazzaville na kasar KwangoHoto: Pacome Pabandji/AFP/Getty Images

Ta ce Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta dauki muhimmin mataki don kawo karshen dambarwar siyasa a kasar bayan da majalisar dokoki ta wucin gadi a birnin Bangui ta amince da sabon daftarin wanda al'ummar kasar za su kada kuri'a kai a ranar 4 ga watan Oktoba, sannan zabukan 'yan majalisar dokoki da na shugaban kasa su biyo baya a ranar 18 ga watan na Oktoba, kana idan ta kama a gudanar da zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a ranar 22 ga watan Nuwamba, sannan sabuwar gwamnatin da za a zaba, za ta kama aiki a farkon shekarar 2016. Daftarin tsarin mulkin ya kuma tanadi wa'adin mulki sau biyu wanda kuma ba za a iya masa kwaskarima ba. Rashin mutunta wannan sashe na doka na zama daya daga cikin dalilan hambarar da shugaba Francois Bozize a shekarar 2013.

Illa ga muhalli daga dagwalon kayayyakin lantarki

Daga batun rikicin siyasa sai na muhalli a kasar Ghana, inda jaridar Berliner Zeitung ta ce unguwar Agbogbloshie da ke Accra babban birnin kasar ta kasance wani jujin dagwalon tsoffin kayakin lantarki mafi girma a duniya, wanda yawancinsu ba sa aiki kuma ke tattare da sinadarai masu guba ga lafiyar dan Adam. Jaridar ta ce kasancewa a irin wuraren tara sharar tsoffin kayayakin lantarkin na samar guraben aiki ga dinbm jama'a ya sa gwamnatin Ghana na dari-darin daukar wani matakin rufe wurin duk da illolin da yake janyo wa mutane da muhallinsu.