Dakon hukunci kan cinikin jarirai a Jamhuriyar Nijar
May 11, 2015Mutane 32 ne dai ake tuhuma kan wwannan batu ciki kuwa har da tsohon shugaban majalisar dokokin kasar Hama Amadou da a yanzu haka ke gudun hijira a kasar Faransa. Lauyoyin da ke kare wadannan mutane sun ce babu wanda ya bayar da rahoton sace masa jariri daga Najeriya, wanda hakan ya sanya cikin watan Janairun da ya gabata alkalin da ya fara sauraron shari'ar ya ce ba shi da hurumin sauraron wannan shari'a.
Alkalin alkalan kasar wanda shine ke wakiltar bangaren gwamnati da ya daukaka kara Ibrahim Boubakar Zakariya ya ce ya na fatan kotun daukaka karar za ta yi watsi da hukuncin farko da kotu ta yanke cikin watan Janairun da ya gabata. A nasu bangaren lauyoyin da ke kare Hama Amadu bukatar kotun suka yi ta soke dokar sammacin kamo shi da gwamnati ta bayar tun ranar daya ga watan Yulin 2014. Wakilinmu na Yamai Mahaman Kanta ya ruwaito cewa a ranar 13 ga watan Yuni mai zuwa ne kotun ta ce za ta yanke hukunci a wannan shari'ar.