Shari'ar Bosco Ntaganda a Kotun ICC
September 3, 2015Lauyoyin shugaban 'yan tawayen nan Bosco Ntaganda sun karyata zargin da ake mi shi na cewa shi ne ya janyo ajalin mutane da dama, inda suka ce a maimakon haka, ya kamata a yi la'akari da cewa shi soja ne wanda ya yi iya kokarinsa na kare fararen hula a kasar Kwango.
Labaran fyade da kissan kiyashinm da suka afku a yankin Arewa maso gabashin Kwangon, tsakanin shekarun alif dubu daya da dari tara da farkon dubu biyu ne suke daukar hankali a shari'ar da aka yi wuni biyu ana yi yanzu, wanda masu shigar da kara ke zargin cewa Ntaganda ya hada rundunar mayaka, domin karfafa magoya bayan shi ta yadda za su sami karfin anshe albarkatun kasar su mayar da su a karkashin mallakarsu. Daga farkon shari'ar daya daga cikin lauyoyin iyalan da abin ya shafa ya kwatanta yadda aka rika cin zarafin mata wadanda ke da shekaru 12 zuwa kasa.