1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka a Jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar AMA
July 23, 2021

Kafa kamfanin sarrafa allurar rigakafin corona na farko a Afirka da barkewar tarzoma a Afirka ta Kudu sun ja hankalin jaridun Jamus a sharhukan da suka rubuta a wannan mako.

https://p.dw.com/p/3xv0x
Symbolbild Pressespiegel
Wasu daga jaridun Jamus masu sharhi kan nahiyar AfirkaHoto: Jan Woitas/dpa/picture alliance

A labarinta na wannan makon da jaridar "Handelsblatt" ta wallafa mai taken "Nan ba da jimawa ba allurar rigakafin BioNtech za ta isa Afirka". Jaridar ta ce Biovac na zama kamfanin sarrafa magunguna Afirka na farko da zai aikin hadin gwiwa da kamfanonin BioNtech da Pfizer.

Sanarwar da ta fito daga kamfanonin na nuni da cewar, nan ba da jimawa ba nahiyar ta Afirka za ta fara samun alluran na BiNtech kai tsaye, biyo bayan aikin hadin gwiwar da ke gudana da kamfanin Biovac na kasar Afirka ta Kudu.

Ba wai kamfanin na Biovac zai sarrafa magungunan kadai ba, amma zai taimaka wajen rabon alluran a dukkan kasashen Kungiyar Tarayyar Afirka 55. A shekara mai zuwa ne dai ake saran kamfanin zai fara sarrafawa tare da rarraba alluran. Kuma idan har Biovac din ya fara cikakken aikin sarrafa allurar, zai iya yin wajen miliyan 100 a ko wace shekara.

Tarzoma ta barke a Afirka ta Kudu

Südafrika , Durban | Plünderungen nahe eines brennenden Warenhauses
Masu zanga-zanga a Durban a Afirka ta KuduHoto: Rogan Ward/REUTERS

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi sharhi kan musabbabin rikicin da ya jagoranci mutuwar mutane masu yawa da asarar dukiyoyi. Jaridar ta ce duk da cewar an dauki wasu 'yan kwanaki da aukuwar wannan rikicin, har yanzu al'ummar Afirka ta Kudun sun kasa tantance adadin asarar da suka yi. An fasa shaguna wajen 800 inda aka kwashe dukkan kayan cikinsu, a yayin da aka lalata wasu shaguna 200, daura da wadanda aka kone kurmus. An kone rumbunan ajiyar kayayyaki.

Mazauna gunduwowin Durban da Johannesburgh sun tabka asarar da ta ritsa har da ginin makarantu.  Sama da mutane 200 nedai suka raya rayukansu a tarzomar da ta barke a yankunan kasar guda biyu, tun bayan da kotu ta iza keyar tsohon shugaba Jacob Zuma zuwa gidan yari.

Jami'an soji da na 'yan sanda wajen dubu 25 ne dai shugaba Cyril Ramaphosa ya aike domin kwantar da rikicin, godiya ga wasu 'yan kasa na gari da suka taimaka wajen kawo karshen rikicin cikin gajeren lokaci. Sai dai ya zuwa yanzu babu wanda ya san wadanda suka tada rikicin, da wasu ke dangantawa da masu adawa da shugaba Ramophosa.

Cutar corona ta yi nakasu ga yaki da HIV

HIV AIDS in Afrika | Simbabwe Harare Medikamente
Magungunan da masu HIV ke amfani da suHoto: Jekesai NJIKIZANA/AFP

Jaridar Neues Deutschland labari ta yi mai taken "Annobar da aka mance da ita". Jaridar ta ce masu kamuwa da cutar HIV na fuskantar barazanar mutuwa daga annobar corona, don haka ana bukatar karin alluran rigakafi a kasashe matalauta.

Barkewar annobar corona ya mayar da hannun agogo baya dangane da manufar Majalisar Dinkin Duniya na rage yawan masu dauke da cutar HIV ko AIDS nan da shekara ta 2030, amma kuma annobar wata makaranta ce ta daukar darasi, kamar yadda taron kasa da kasa na kwararru a fannin kimiyya ya nunar.

Matakin takaita zirga-zirga ko lockdown da sauran matakan yaki da corona ya haifar da nakasu a yakin da ake yi da HIV, a cewar Majalisar Dinkin Duniya a wani sabon kiyasin da aka gabatar a birnin Geneva a makon da ya gabata. Alal misali, dokokin yakar corona a wasu kasashen sun takaita gwajin HIV da ma yadda za a kula da masu dauke da cutar zuwa gaba. A yankin KwaZulu-Natal da ke kasar Afirka ta Kudu alal misali, an rage gwajin zuwa rabi, saboda matakan takaita zirga-zirga a karon farko a watan Afrilun shekarar 2020 da ta gabata. 

An karkatar da ma'aikatan jinya da ke kula da masu dauke da cutar HIV, zuwa masu kula da masu Covid 19. Rashin samun allurar rigakafin coronar babban hadari ne ga masu dauke da manyan cututtuaka kamar HIV da cutar sukari da makamantansu. Dangane da haka ne kwararru ke kira ga kasashe masu arziki da su kwatanta adalci wajen rabon alluran riga kafin domin ya kai ga kasashe matalauta da basu da sukunin samu, don ceto rayukan al'umma musamman wadanda ke cikin hadarin rasa rayukansu idan sun kamu da cutar COVID-19.