Sharhunan Jaridu: 15.11.2024
November 15, 2024Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce gwamnatin Kasar Mali ta tsare manajan wani kamfanin hakar ma'adinai. Jaridar ta ci gaba da cewa gwamnatin Mali da ke yammacin Afirka sai kara daukar tsauraran matakai ta ke bisa kamfanionin kasashen yamma. Inda a yanzu kasar Mali ke nuna cewa hukumomin kasar ne ya kamata su zama kan gaba a hakar ma'adinan kasar su ba wai wasu kasashen Turawa ba. Matakn na gwamnatin Mali na baya-baya nan sun shafi kamfanin hakar ma'adin kasar Ostiraliya ne mai suna Resolute, wanda hukumomi suka tsare manajan kamfanin wanda ke hakar ma'adinai a yankin Syama mai arzikin zinari.
Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta yi labarinta ne kan kasar Sudan tan kudu, inda jaridar ta ce kimanin mutane 400.000 ambaliyar ruwa ta shafa. A cewar MDD, wadannan mutane 400.000 duk a yanzu ambilyar ruwa ta yi sanadin rasa gidajensu. Jaridar ta ci gaba da cewa kasar da dama can ba ta da ma'aikatun masu karfi da ke kula da jama'a, yanzu haka karuwar wadanda ke kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro ya kai wani matakin ba dadi, kuma ga shi karin rashin muhalli wanda zai kara kawo wasu cututtuka. Daman can ma'aikatr kiwon klafiya a Sudan ta Kudu masu jinya sun fi karfin asibotcin, don haka ayyukan jinkai sun yi matukar karuwa yayin ambaliyar mai muni.
A wani labarin da jaridar ta Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta yi shi ma ya shafi kasar Sudan ne, inda Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta ce kisan gilla kan fararen hukla na kara muni a kasar Sudan mai fama da yakin basa-sasa. Kuma wannan yakin na farauwa ne a kasar da yanzu haka ke da matukar wahalar isar da kayan agajin jinkai ga masu bukata. Jaridar ta ce yanzu haka sama da mutane miliyan 10 suka tserewa yakin, abinda ya kawo munnunar wahala ga fararen hula.
Ita kuwa jaridar die tageszeitung ta duba kasar Senegal ce, wacce ke gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki. Jaridar ta ce yayin da 'yan siyasa ke kai kawo na neman muklamaia saben, su kuwa matasan Senegal sai kara koyon dabarun tsallakawa izuwa kasashen Turai suke yi. Shuagaba da ke kan mulki ya rusa majalisar dokokin Sengal da aka zaba kasa da shekara guda, kasancewar ba shi da rinjaye a majalisar yanan ganin yin aiki da majalisar da yan adawa suka mamaye yana da wuya, don haka a wannan zaben jam'iyya mai ci ta samu rinjaye.
Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi makamancin wannan labarin, inda ita kuwa ta duba kasashen Larabawa da ke arewacin Afirka. Neue Zürcher Zeitung ta ce ta yiwu a samu karin matsa daga kasashen Tunisiya, Moroko da Aljeriya wadanda za su ci gaba da tsallakawa izuwa Turai don samun rayuwa mai inganci. A ziyarar da jaridar ta kai gabar ruwan tekun Bahrum ta ga yadda matasan arewacin Afirka ke hawa kan kwale-kwale kamar wasa suna daukar hotuna kafin su kama hanyar mai hatsari ta tsalklakawa izuwa Turai, kuma kasancewa rashin tsarin demokaradiyya mai inganci, babu wata alamar hukumomin irin wadannnan kasashen za su kyautata mulkinsu wanda zai sa matasa sun fahimci suna da makoma a cikin kasashen su.