1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Jamus ya janyo sabon kiki-kaka

Pohl Ines Kommentarbild App
Ines Pohl
September 25, 2017

Wannan zabe ya kasance wani sauyi ga siyasar Jamus sakamakon yadda jam'iyyar kyamar baki ta AfD ta samu shiga majalisa a cewar babbar edita ta DW Ines Pohl a cikin wannan sharhi da ta rubuta.

https://p.dw.com/p/2ke36
Deutschland Bundestagswahl | Merkel
Hoto: picture alliance/dpa/B. Roessler

Ines Pohl ta ce wannan zabe wani sako ne karara, wanda kuma bai wuce a fadi haka ba kawai. Kana wadanda suka yi asara a zaben su ne SPD da Angela Merkel, ganin irin yadda sakamakon jam'iyyar SPD ya zamanto mafi karanci a tarihin siyasar na kashi 20.8 cikin 100, yayin da ita kuma jam'iyyar Angela Merkel ta CDU ta rasa kusan kashi takwas cikin dari na sakamakon da ta samu a baya abin da kan iya kamantawa da cewar wata girgizar kasa ce ga jam'iyyar.

Hasalima yadda abubuwan suka birkice a lokaci daya, jam'iyyar da ke da hakidar kyamar baki ta AfD ta samu kashi 12.6 a zaben 'yan majalisun dokokin na Bundestag wanda kuma shi ne karo na farko wata jam'iyya ta masu tsatstsaura ra'ayi ta shiga majalisar dokokin ta Bundestag tun girka gwamnatin tarayya.

Wani sauyi mai tarihi aka cimma da wannan zabe, a game da yadda kasar ta zama wata daban, amma dai duk da haka ba wani karamci ne ba, ko kuma bala'i. A karshe dai kalubale ne kuma demokaradiyya ce haka ta gada. Sannan duniya baki daya na yi wa Jamus kallon cewar za ta iya fuskantar kalubalen har ma ta ciwo kansa. Inda har gwamnatin za ta samu kwarin gwiwa da hadin kai a majalisar dokokin. Sai dai babu wata daga cikin gwamnatin ta Jamus da ta fuskanci irin wannan lamari na yanzu da ka iya zama adawa mafi karfi da ba a taba gani ba.

Herbsttreffen der Medienfrauen 2017 Ines Pohl
Hoto: DW/P. Böll

Akwai bukatar cewar jam'iyyun siyasar sai sun yi hattara, domin kada su kuskura su fada cikin tarkon jam'iyyar ta AfD a game da irin jawabai na siyasa da take yi, don sai sun nuna karfin hali da jajircewa don kaucewa fadawa cikin rudanin 'yan siyasar masu tsatstsaura ra'ayi. A maimakon haka abin da ya kamata shi ne na kokarin samar da hanyoyin magance matsalolin da ke da akwai, Kuma wani abin da ya dace a lura da shi shi ne cewar jama'a da dama na da fargaba a game da batun bakin haure ta yadda za su iya kawo canjin al'amura a cikin kasarsu. Dole Jamusawa su yi tunani da irin jawaban da aka saba yi cewar jin tsoro na wasu abubuwan da ba a son bayyanawa na karfafa gwiwa ga masu tsatstsaura ra'ayin.

Jam'iyyar SPD ta shiga adawa

Babban kalubale na farko a yanzu shi ne na kafa gwamnatin gamin gambiza. Za a iya fahimtar kalaman jam'iyyar SPD wacce ta yanke za ta yi adawa, domin ta haka kwai za ta iya kai ga samun wata sabuwar alkibla don kyautata makomarta a gaba. Sannan da ba za a iya hanawa jamiyyar AfD ba zama babbar jam'iyyar adawa a majalisar dokokin ta Bundestag.

Angela Merkel dai ta damu da abin da ke gabanta na yin tattaunawa mai sarkakiya da sauran jam'iyyun siyasar wadanda suke da manufofi a kan batutuwa daban-daban bugu da kari kan shirinta na karbar 'yan gudun hijira wanda ke cike da cece-kuce, wanda ko a cikin sahun jam'iyyar ta CDU tana da abokanan adawa.

Wani abu na daban kuma shi ne cewar duniya na tsamanin cewar duk da irin wannan sakamako da aka samu. Angela Merkel ta kasance daya daga cikin shugannin 'yan siyasa na Yammancin Duniya wacce tare da ita Jamus ta kasance abokiyar hulda dorarriya kana kuma tabbas a duniya, ganin irin yadda demokaradiyya ta girku a kasar wanda  kowacce daga cikin jam'iyyun siyasar har ma da AfD sun san cewar mutuncin dan Adam abu ne da ba za a iya keta shi ba, wanda doka ce da ke a cikin kudin tsarin mulkin kasar.