Sharhi: Trump ka iya yin tazarce
August 28, 2020Cikin sharhinta da ta rubuta, shugabar ofishin tashar DW a birnin Washington Ines Pohl ta ce yanzu da Donald Trump ya karbi takara, yakin neman zabe zai kankama da yada karerayi da sanya tsoro a zukatan al'umma da kuma rudani, koda yake ta ce a karshe tana iya yiwuwa a sake zabarsa. Ines Pohl ta ce Trump ya kammala babban taron jam'iyyar ta Republican tare da amincewa da tsayar da shi takara da jam'iyyar ta yi.
Zaben Amirka da matsin tattalin arziki
A jawabin da ya gabatar a kan wani katon dandamali a wajen fadar White House, ya ce ya karbi amincewar da jam'iyyar ta yi masa da kyakkyawar zuciya mai cike da godiya da kwakkwaran kudiri, sannan ya bayyana zaben da ke tafe a matsayin mafi muhimmanci a tarihin kasar. Da yake sukar Joe Biden da ke zaman abokin hamayyarsa, Trump ya ce Biden bai taba zama zabi mafi dacewa a tsakanin jam'iyyu biyu ko kuma a tsakanin tafarki guda biyu ba. Yana mai baiyana manufofin jam'iyyar Democrat a matsayin mafi tsaurin ra'ayi da wata babbar jam'iyya ta taba gabatarwa. Ya ce Biden ba zai iya ceton Amirka ba sai dai lalata ayyuka a Amirka, kuma idan aka ba shi dama zai rusa ci-gaban Amirka da martabarta.
Ines Pohl ta ce Trump ya lashi takobi sai ya ga bayan annobar corona, inda yace labudda Amirka za ta samar da allurar rigakafi nan da karshen shekara ko ma watakila nan kusa. Ya yi alkawarin cewa kasar za ta sami gagarumin ci-gaba idan aka sake zabarsa, yana mai alwashin sake raya kasar ta Amirka mafi karfin tattalin arziki a duniya. Da ya juya ga tarzoma game da rashin daidaito a tsakanin jinsin al'umma, ya ce babu wani shugaba da ya kyautata wa Amirkawa bakar fata kamarsa, inda ya yi alkawarin cewa karin kyautatawa ma sai nan gaba.
Zaben Amirka: Wacece Kamala Harris?
Ta ce ko da yake abubuwa da dama da Trump ya fada ba gaskiya ba ne, amma akwai yiwuwar ya ja ra'ayin masu kada kuri'a wadanda har yanzu ba su yanke shawarar wanda za su zaba ba, inda ya nuna cewa yana da gagarumin shiri a kan corona da batun tattalin arziki da kuma yadda yake tunkarar Chaina da a cewarsa Biden bai yi hakan ba. Ya yi alkawarin cewa idan aka zabe shi, to kuwa za a ga ci-gaba sosai a Amirka. Amincewa da takarar tasa dai, na zuwa ne bayan tsawon kwanaki na tashe-tashen hankula a Winsconsin sakamakon harbin da 'yan sanda suka yi wa wani bakar fata Jacob Blake da baya dauke da makami a Kenosha, yayin da ya je zai shiga motarsa.
Mataimakin shugaban kasar Mike Pence shi ma a jawabinsa yayin da yake amsa tsayar da shi takara, ya kare 'yan sandan, inda ya bukaci kawo karshen tarzoma a biranen da aka sami tashin hankali yana mai cewa a karkashin shugabancin Trump har abada ba za a hana 'yan sanda kudi domin gudanar da ayyukansu ba.
Gallazawar 'yan sanda a wasu sassan Afirka
Bakake da dama dai sun yi jawabai a taron, wadanda suka hada da Kim Klacik wanda zai tsaya takarar dan majalisar dokoki a Baltimore da sakataren gidaje da raya birane Ben Carson da kuma baki mafi girman mukami a fadar White House JaRon Smith. A yayin wata gidauniyar tara kudi a ranar Alhamis, Biden ya caccaki Trump inda ya ce yana amfani da tarzoma a matsayin wata dabara ta siyasa maimakon ya mayar da hankali wajen warware matsaloli.
Trump dai ya sha nanata cewa Amirka ba za ta sami kwanciyar hankali tare da Joe Biden a matsayin shugaba ba, shaidar hakan kuwa ya ce shi ne halin da kuke gani a yanzu. Yayin da a nasa bangaren Biden ya ce tarzomar da ake gani, na faruwa ne a gwamnatin Trump inda ya kare da tambaya yana mai cewa shin ko kun manta wanene shugaban kasar?