Tun cikin watan Disambar shekarar da ta gabata ce shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kira wani zama na musamman a birnin Pau da ke kudancin Faransa don tattaunawa da shugabannin kasashen nan biyar na yankin Sahel da suka hada Burkina Faso da Mali da Chadi da Mauritaniya da kuma Niger don tattaunawa kan halin da yankin ke ciki, sai dai gab da fara taron aka dage shi saboda harin da 'yan ta'adda suka kai wani sansanin sojin Nijar. To sai dai a share guda wasu na ganin dage taron da aka yi na da nasaba da yadda aka gayyaci shugabannin, wanda da dama ke cewar abu ne da ya yi kama da aikewa da sammaci garesu na su bayyana a Faransa din don tattaunawa da Macron.
Dangantaka dai tsakanin Faransa da kasashen Afirka na da 'yar sarkakiya. Ana dai yi wa ita wannan dangataka lakabi da Françafrique, wadda aka ginata kan yin aiki tare da masu fada a ji a nahiyar da 'yan kasuwa. 'Yan kasashen Afirka da Faransa ta yi wa mulkin mallaka dai na kallon wannan hadaka a matsayin wata dabara da Faransa ke amfani da ita wajen wawashe dukiyar da kasashen Afirka ke da su. Baya ga wannan, alakar kuma ta fuskanci aiki tare ta fuskar tsaro wanda ke da wuyar gaske. Wannan ne ma ya sanya shugabannin kasar na baya suka nesanta kansu da wannan tsari na Françafrique.
Faransa ta kara yawan sojojinta a Sahel
To sai dai duk da haka danganta tsakanin Faransa da kasashen da ta yi wa mulkin mallaka na ci gaba da wakana ta fuskar siyasa da tattalin arziki da kuma tsaro domin sojojin kasar na daga cikin wadanda ke aiki a rundunar nan ta Majalisar Dinkin Duniya ta Minusma a Mali, wadda ke aikin wanzar da zaman lafiya. Sannan ta kuma tura sojojinta kimanin dubu hudu da dari biyar don yaki da 'yan ta'adda karkashin rundunar nan ta Barkhane.
Dangantaka tsakanin Faransa da kasashen Sahel ta fuskar yaki da talauci ma dai na da karfi sosai kuma shugabannin kasashen da suka halarci taron birnin Pau na Faransa kan sha'anin tsaro na son ganin dangantakar ta dore duk kuwa da cewar wasu ba sa goyon bayan hakan. Tuni dai bangarorin biyu suka amince da girka wata runduna ta musamman don yakar ta'addanci kuma Faransa ta yi alkawarin aikewa da sojinta 220 don ba da gudunmawa.
Duk da cewar kasashen sun yi hadaka kan abu guda wanda shi ne yakar ta'addanci, da wuya su kadai su iya cimma burinsu a yakin na Sahel, saboda rashin kwarewa da sojojin yanki ke da ita, baya ga karancin kudi na aiwatar da ayyukansu. Haka ma abin yake ga jami'an 'yan sanda da fannin kiwon lafiya da bangaren shari'a. Kuma da wannan ne 'yan ta'addar ke amfani da wannan matsaloli da ake da su gami da irin takun saka tsakanin kabilun da ke yankin wajen haifar da husuma, inda suka ja matasa jika tare da kwadaita musu samun abin duniya.
Matakin soji kadai ba zai warware rikici ba
Duk da cewar Faransa na da sojojinta a yanki amma 'yan ta'addar kan kasance sun sha gabansu musamman ma idan aka yi la'akari da irin yadda ake ci gaba da kai hare-hare. Wani bincike ma ya nunar da cewar a shekarar 2019 kadai kimanin hare-hare 700 aka kai wanda suka yi sanadin rasuwar mutane 2000 kuma wannan asarar rai ta al'umma da ake samu da gaza maganceta na daga cikin dalilin da ke sanya dangin wadanda ake kashewa shiga kungiyoyin Jihadi don yin gwagwarmaya da makamai. Shugabannin kasashen da abin ya shafa sun san da haka kuma sun yi maganarsa a taron Pau.
Muhimmin mataki da ya kamata a dauka shi ne neman hanyar warware matsalar ba tare da amfani da karfin soji ba, domin amfani da tsinin bindiga a yakin Sahel da nufin kawar da 'yan ta'adda abu ne mai wuya. Dole ne kasashen su dukufa wajen kula da talakawansu a lunguna da sakunan kasashen ba wai su mayar da hankali kan wanda ke manyan birane ba. To sai dai fa ko da an yi hakan, ba za a cimma nasara ba muddin ba a kawo karshen rikicin Libiya ba domin kuwa ta nan ne manya da kananan makamai ke watsuwa zuwa cikin wasu kasashen Afirka wadanda 'yan ta'adda ke amfani da su wajen kai hare-hare. Faransa dai ta bukaci kara matsa kaimi ta fuskar aikin soja a yankin na Sahel, sai dai Jamus ta yi watsi da wannan kira inda ta ce kyautuwa ya yi a fara warware matsalar da Libiya ke fama da ita tukunna.