1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Nasarar Kagame ba ta zo da mamaki ba

August 7, 2017

Sakamakon zaben shugaban kasar Ruwanda ya nuna cewar Shugaba Paul Kagame ya samu gagarumar nasara kan abokan hamayyarsa. Da dama dai ba su yi mamakin hakan kamar yadda Andrea Schimdt ta bayyana a cikin sharhinta.

https://p.dw.com/p/2hkfk
Ruanda vor den Wahlen 2017
Hoto: Imago/Zumapress/M. Brochstein

A cikin sharhin na ta, Andrea ta ce kundin tsarin mulkin Ruwanda ya bada dama ta kafa jam'iyyu da dama amma kuma masu zabe ba su da wani zabi na a zo a gani a zaben da aka gudanar. Mutum biyu ne dai suka yi takara da Shugaba Kagame wato Frank Habineza na jam'iyyar 'yan rajin kare muhalli ta Green Party da kuma dan takara na indipenda wato Philipp Mpayimana sai dai tun da fari dama ba a dauke su a matsayin wanda za su ja zare sosai da Kagame ba saboda ba a basu dama ta sakewa su yi hakan ba, yayin da a share guda sauran wadanda suka so yin takara suka gamu da cikas tun ma ba a kai ga shiga zaben ba.

Cimma nasarorin cikin yanayi na kama karya

Kagame dai mutum ne da ba ya jurewa adawa sai dai duk da wannan ya taka rawa a fannoni da dama wadanda suka hada da tattalin arziki da kiwon lafiya da kawar da cin hanci kana ya yi kokari wajen rage talauci a kasar. Irin kyakkyawan tsari da tsabtar da Ruwanda ke da ita kan sanya jama'a musamman daga kasashen ketare sanya kasar a kan wani matsayi babba to amma fa idan aka maida hankali kan wasu batutuwa za a ga bakin kasar domin kuwa 'yancin fadin albarkacin baki na cikin yanayi maras kyau kuma ba wani kokari da mahukuntan kasar ke yi na kawo sauyi.

DW Kiswahili | Andrea Schmidt
Andrea Schmidt ta sashin Swahili na DWHoto: DW/L. Richardson

Tazarce na kokarin zama abin yayi a Afirka

Andrea Schmidt ta ce tun bayan da aka kawo karshen kisan kiyashin da aka yi a 1994 ne dai jam'iyyar RPF ke mulki a Ruwanda kuma daga shekarar 2000 kawo yau Kagame ne ke rike da madafun iko. A wancan zaman 'yan kasar da dama da ke gudun hijira sun koma gida domin taimakawa wajen sake gina kasar amma kuma yanzu da dama za su fi ganewa su fice daga kasar. Shin waye zai so zama a kasar da ake sanya idanu tare da karya kashin bayan mutanen da ke sukar gwamnati? A kasashen Afirka da ake yi mulkin kama karya kamar Burundi da Yuganda masu rike da madafun iko sun sauya kudin tsarin mulki don cigaba da zama kan mulki inda suka yi ikirarin cewar su ne kadai za iya tabbatar da tsaro da cigaban tattalin arziki. A Ruwanda ma dai haka aka yi don Kagame ma ya yi haka a shekarar 2015 inda ya shirya kuri'ar raba gardama wadda ta kawar da tsarin da ake da shi na wa'adi biyu kacal ga shugaban kasa a kan gadon mulki.

Neman dama ta yin demokradiyya cikin walwala

Masu tsokaci daga sassan duniya daban-daban kan ce Ruwanda ce kan gaba a kasashen Afirka idan ana magana ta zaman lafiya a halin yanzu saboda haka a iya cewar mulki kama karya ake yi cikin yanayi na zaman lafiya ya fi a ce ana samun tashin hankali to amma ba hujjar da kasashen duniya za su ja bakinsu su yi shiru kan irin abubuwan da ke faruwa a wannan kasa domin kuwa akwai abubuwa da dama da suka kamata a ce an kawar. Alal misali a kullum a kan hana masu sukar Kagame rawar gaban hantsi yayin da wasu 'yan siyasa tuni suka yi gudun hijira inda a gefe guda aka daure wasu ba tare da aikata komai ba yayin da wasunsu kuma suka bace ba amo ba labari.

Bukatar yin matsin lamba ga Kagame da nufin samun sauyi

Yanzu dai Kagame zai fara wa'adinsa na uku kuma a shekaru bakwai din da zai shafe ya na jagorantar kasar fatan da ake da shi bai wuce na samun sassauci ta fuskar gudanar da tsarin demokradiyya cikin 'yanci da walwala ba da samun 'yancin fadin albarkacin baki kana a kyale kungiyoyin fararen hulu su mike kafafunsu saboda a zabe na gaba da za a yi a shekarar 2024 'yan takara da dama su iya shiga a dama da su. Domin ganin tabbatar wannan fata, dole ne fa a matsa lamba ga Kagame na ya bada sarari faruwar hakan musamman ma daga kasahen ketare.