1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Matakan ceto kasar Girka da kudin hadin gwiwa na Euro

October 4, 2011

Gwamnatin Girka ta ce tana bukatar taimakon kudi na gaggawa abin da ya kai Euro miliyan dubu takwas ko kuma ta kasa samun damar biyan albashin ma'aikatan gwamnati da fenshon tsoffin ma'aikata.

https://p.dw.com/p/12leX
Kudin Euro na cikin halin tsaka mai wuya

A takaice dai Girka tace ba zata iya biyan albashin ma'aikatan gwamnati ko kudin fensho ba. A daura da haka, ministocin kudi na kasashe 16 da suka rage masu amfani da Euro, sun nuna cewar Girka bata bukatar wani taimakon kudi sai a watan Nuwamba mai zuwa. Sun kuma sanar da cewar Girka din wannan taimako ma ba zata same shi ba, sai ta kara kwazo a matakan ta na tsimi.

Masu iya magana sukan ce wai kudi masu gida rana, yayin da a fannin tattalin arziki, masana sukan ce wai mafi yawan harkokin kudi akan yi su ne da ka. A game da dangantakar kudi dake tsakanin Girka da sauran kasashen Turai, akwai alamu fannin tattalin arziki bashi da muhimanci, inda aka fi maida hankali ga matsin lambar siyasa. Tun a farkon lokacin bazara aka gane cewra Girka ba zata sami nasarar cimma burin ta na cike gibin kasafinkudin kasar ba. Abin da aka kasa fahimta shine, yadda tun a wannan lokaci, kasuwannin hada-hadar kudi suka kasa maida martani game da wannan hali da Girkan ta kasance a ciki. Bankin Dexia na hadin gwiwar Faransa da Belgium da sauran bankunan dake rike da hannayen jarin kasar Girka, sun kasance cikin wani hali na matsin lamba saboda rashin hangen yanayin da Girka din zata kasance a ciki. Saboda haka aka rika kwatanta taimakon da kasar take samu domin shawo kan dimbin bashin dake kanta, kamar dai abin da akan ce ne wai barin kashi a ciki. Zuwa gaba ko Girka din zata iya biya ko ba zata iya biya ba, amma masu binta bashi zasu nemi kudin su daga gareta.

2011 Griechenland Finanzkrise Proteste Athen
Zanga-zangar adawa da matakan tsimi na kasar GirkaHoto: dapd

Tun a watan Nuwmaba mai zuwa ya kamata a yi wa Girka sabon tsari na yadda zata biya dimbin bashin dake kanta, wanda hakan ma shi ya sanya kasashen na Turai suke dari-dari a game da kara mata wani sabon bashi, ba tare da sun ga alamun zata biya wanda tuni yake kanta ba. Kafin a amincewa Girka din da wannan sabon mataki, tilas sai an tuntubi masu binta bashi an sami amincewar su. Wadannan masu binta bashi kuwa sune bankuna na Turai da na Amerika, ko kuma musamman babban bankin Turai da bankuna masu zaman kansu da suke rike da hannayen jarin kasar ta Girka. Sai dai kuma a zahiri daidai lokacin da kungiyar hadin kan Turai da bankin duniya suke ci gaba da kokarin ceto kasar Girka daga halin da take ciki, amma babban abin da masu wannan kokari suka damu dashi shine su ceto tsarin aiyukan bankuna a nahiyar ta Turai kawai. Duk da haka, ba dukkanin bankunan Turai ne za'a iya ceto su daga matsalar da suka fada ta kudi ba. Wasu daga cikinsu, kamar dai bankin Dexia, zai kasance a jerin bankunan da tilas masu biyan haraji a Turai su karbi alhakin tafiyardasu, ta hanyar taimako na musamman daga kasashe 17 dake amfani da kudin hadin gwiwa na Euro. Wasu kasashe, cikin su har da Holland da Slovakia har yanzu basu sanya hannu kan yarjejeniyar kara yawan kudin taimakon gaggawa na kasashen Turai ba, wato EFSF a takaice.

Ranar 17 ga watan Oktober shugabannin kasashen Turai zasu sake hallara domin gudanarda wani taron koli tsakanin su, inda tilas a wannan lokaci su yanke kudiri a game da matakan da zasu dauka game da ceto kudin na Euro.

Mawallafi: Riegert/Aliyu

Edita: Usman Shehu Usman